Zan tsaya takarar dan majalisa a 2019

0

Shaharren jarumin Kannywood, Lawal Ahmad ya bayyana aniyar sa na tsayawa takarar dan majalisar wakilai mai wakiltar Bakori/Danja a zabe mai zuwa na 2019.

Jarumin ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Premium Times ta yi da shi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce ya yanke hukunci tsayawa takarar ne a sakamakon irin goyon bayan da ya ke samu daga mazabar shi.

Ya ce duk da cewa a Kano ya ke da zama, ya na yawaita ziyarar mazabar ta shi, inda ya ke haduwa da mutanen shi.

Ya ce ya samu kiraye kiraye da dama daga wajen su domin ya dawo gida ya yi takara.

A cewar Ahmad “Ina jin dadin taimakawa jama’a, kuma na yi wa jaha ta da mutane na abubuwa da dama da ba zan iya bayyana wa ba a nan.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Da aka tambaye shi ko ya na tunanin zai iya buge dan majalisa mai ci, Ahmad ya ce ya barwa Allah wannan.

Shi dai ya san zai yi takara kuma zai samu goyon baya daga wajen mutanen shi, wanda hakan ne ke bashi karfin gwiwar zai samu nasara.

Yayin da 2019 ke karatowa, jarumin ya ce ya fara shirye shirye da tawagar shi, yayin da ye ke amfani da damar wajen fahimtar abubuwan da siyasa ta kunsa.

A cewar shi ” Na yi imanin zan yi nasara”

Source:24wikis