Zan mika kaina ga sojin Nigeria

0 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ɗan jaridan nan da rundunar sojin Nigeria ta ke nema ruwa-a-jallo, Ahmed Salkiɗa ya ce zai mika kansa a ‘yan kwanaki masu zuwa. Salkiɗa wanda a halin yanzu ya ke zaman gudun hijira a Dubai ya shaida wa BBC cewa, zai gaggauta zuwan nasa idan da rundunar sojin za ta aika masa da tikitin jirgi. Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cigiyar Salkiɗa da Ambassada Ahmed U. Bolori da kuma Aisha Wakil ne bisa zarginsu da boye wasu muhimman bayanai game da kungiyar Boko Haram. Kakakin rundunar, Kanar Sani Usman ya gaya wa BBC cewa mutanen uku na da kusanci da Boko Haram, amma suka ƙi bai wa hukumomi bayani game da ‘yan matan Chibok da ƙungiyar ta sace. A wani sakon da ya turowa BBC, Salkida ya ce a matsayinsa na dan jarida yana aikinsa ne ba tare da keta dokokin aikin ba. Kuma sau uku gwamnatin Najeriya na gayyatarsa zuwa kasar a shekarar 2015, domin taimakawa a saki ‘yan matan na Chibok, yunkurin da ya ke kallo a matsayin wani sadaukar da kai ne daga bangarensa. Mista Bolori ya musanta zargin, kuma ya shaida wa BBC cewa ya kai kansa amma rundunar ta ce ya koma gida sai ranar Litinin tukuna. Ita kuwa Aisha Wakil ba ta ce komai ba kawo yanzu. Ahmad Salkida, yana da kusanci da Boko Haram, kuma shi ne ke wallafa yawancin bayanansu a mafi yawan lokuta. Kungiyar na tura masa faifan bidiyo da hotuna kai tsaye, amma sai dai ya ce su da kansu suke wallafa bidiyonsu a yanar gizo. A lokacin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi kokarin shiga tsakanin gwamnati da Boko Haram domin ceto ‘yan matan Chibok, amma yunkurin bai yi tasiri ba. A wata hira da ya yi da BBC a bara, Salkida, ya musanta cewa yana da alaka da kungiyar, yana mai cewa aikinsa kawai yake yi na jarida.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.