Zai yi wuya na koma fitowa a fina-finai

0

Tsohuwar jaruma, kuma shahararriyar jaruma a kamfanin shirya fina-finan Kannywood Mansura Isa ta ce ba ta jin
damuwa akan rashin fitowa a fina-finai saboda sai da ta kai kololuwar ganiyarta kafin ta daina yin fim.

A cewar ta bata kewar bayyana a fim domin sai da ta kai kololuwar ganiyar ta kafin ta bar dandalin.

Ta kara da cewa ta mallaki muhimman abubuwa da kuma nasarori da dama tace : “na
gina gida na kaina, na sayi mota, na je Umra, hasalima na auri gwarzon
jarumin Kannywood.

“Me zan ce bayan haka idan ba godiya ga Allah ba “, cewar Mansura a zantawa da ta yi da jaridar yanar gizo na Premium Times.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Tsohuwar jarumar, wacce ta kasance edita ta farko a masana’antar Kannywood, ta kara da cewa ta daina fitowa a fina-finan ne lokacin da ta yi aure saboda ta maida hankali ga iyalinta.

A cewarta, yanzu ba ta kallon fina-
finan Kannywood saboda ba ta da
isasshen lokaci na yin hakan.

Ta ce zai yi wuya ta koma fitowa a fina-finai saboda yanzu tana gudanar da wata gidauniya.

©naij.hausa.com