Za’a Bayana Wanda Yacci Zaben Bauchi

0

Hukumar zaben Nijeriya mai zaman kanta INEC ta ce za ta ci gaba da tattara sakamakon zabe na mazabu da rumfunan zabe domin hada sakamakon karamar Tafawa Balewa a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki na jiha.

Hukumar ta nada sabon jami’in zabe da zai ci gaba da tattara sakamakon, wanda kuma zai maye gurbin tsohuwar jami’ar tattara sakamakon wacce ta janye daga aikin saboda barazana da tace tana fuskanta.

A makon jiya ne hukmar zaben ta Najeriya INEC ta bayyana cewa zaben jihar Bauchi bai kammala ba, kuma za a sake zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, saboda rashin samun sakamakon zaben kamar yadda dokokin zabe suka tanada, bayan tashin hankali yayin tattara sakamakon.

KARANTA WADANNAN;
1 of 93

INEC ta ce za ta yi amfani da kwafin takardun da aka rubuta sakamakon zaben a kansu a mazabu, wadanda daga nan za a samu sakamakon karamar hukumar.

Sannan hukumar ta ce gano cewa akwai kuskure wajen lissafin kuri’un da aka soke a rumfuna hudu a karamar hukumar Ningi inda aka ce sun kai 25,330, maimakon 2,533 wadanda INEC din ta ce su ne alkaluma na gaskiya.

Hukumar ta ce a yanzu za a sake lissafi da alkaluma na gaskiya na kuri’un da aka soke a karamar hukumar Ningi da suke 2,533.

#bbchausa