Yarinya ‘Yar Shekaru 10 Ce Ta Kai Harin Kuna Bakin Wake a Maiduguri

0

Wata karamar yarinya da aka kiyasce shekarunta ba su wuce goma ba ita ta kai harin kunar bakin wake a Maiduguri, inda ta tarwatsa kanta a wani yunkurin kai hari akan wata matattarar jama’a. Wadanda abun ya faru a gaban su sun shaidawa manema labarai cewa yarinyar ta tarwatsa damarar bom din da ke jikinta dan taki kadan kafin ta kai inda ta yi niyyar tayar da bon din, wato wani matattarar cin Indomie da ke kusa da ofishin kwastam da ke nan Maiduguri.

Mutane da dama na ganin tsoro ne ya sa ta tayar da bom din kafin lokaci. Nan dai take yarinyar ta rasa ranta, a yayin da kuma wani mutum guda ya yi mummunan rauni
sakamakon tartsatsin fashewar bom din.

Wadanda abun ya faru a gabansu sun saida cewa yarinyar ba ta wuce shekaru 10 ba bayan da suka duba gawarta.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Wannan abu dai ya faru a ranar Asabar da ta gabata, ranar jajiberin bukukuwan New year kuma mako daya kacal bayan da shugaban kasa Buhari ya sanar ta fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram daga dajin Sambisa.

Yanzu haka dai, jami’an tsaro na ci gaba da gargadin mutane da su zama masu lura da zuba ido saboda irin wadannan ‘yan kunar bakin waken da suka bazu cikin jama’a bayan da aka tarwatsa sansaninsu a dajin Sambisa.