Yar Somalia ta zama yar majalisa a Amuruka

0 1

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Ilhan Omar ta kafa tarihi bayan da ta zamo ‘yar Somalia ta farko da aka zaba a matsayin ‘yar majalisar dokoki a Amurka.

Ms Omar, wacce aka haifa a Somalia, ta je Amurka
ne a matsayin ‘yar gudun hijira.
An zabe ta a majalisar wakilai ta jihar Minnesota a wani zabe mai zafi da aka fafata bara.

Zaben Ms Omar, wacce Musulma ce, ya zo kwanaki kadan bayan da zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi ‘yan gudun hijirar Somalia a Minnesota da “yada tsattsauran ra’ayi”.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Akwai al’ummar Somalia da dama da ke zaune a Amurka, musamman a jihar Minnesota.

Kuma ana yi wa zaben Ms Omar wani kallon abin da ka iya kara fito da kimar ‘yan kasar da ke zaune a jihar da ma Amurka baki daya.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram