Yan sanda sun cafeke mutumin da yasawa karen sa suna Buhari

0 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

‘Yan sanda sun cafke wani dan kasuwa mai shekaru 30 dan Jahar Ogun a sakamakon karar sa da wani makocinsa bahaushe ya kai na cewar ya ci zarafin sunan babansa Alhaji Buhari. Dan kasuwan mai suna Joe Fortemose Chinakwe ya sanyawa karensa suna Buhari kuma ya rubuta sunan a kowani gefe na jikin karan. Banda haka ya kan yi yawo da shi a yankunan da hausawa suka fi zama a jahar. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya bayyana cewa laifin da Joe ya aikata shine kokarin tada zaune tsaye da kuma kokarin haifar da rikicin tsakanin kabilu. ‘Yan sanda wanda suka ki bayarda belin Joe sun bayyana cewa za su gurfanar da shi a gaban kuliya, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto. Sai dai an nemi karen an rasa, akwai jita jitan cewa Joe ya umarci abokansa da su kama karen su yanka, idan sun ga dama ma su cinye saboda kar a samu wata hujja akan sa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.