Yan Gudun Hijjira suna bukatar Abinci

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yau ce Ranar Jinƙai ta Duniya, wacce Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware don tunawa da ma’aikatan jinƙai, wadanda ke sadaukar da rayuwarsu don taimaka wa mutanen da ke cikin buƙatar agaji. Najeriya dai na cikin ƙasashen da suka fi yawan ƴan gudun hijira na cikin gida, musamman sakamakon rikicin Boko Haram. Alƙaluma na baya-bayan nan, waɗanda ƙungiyar likitoci ta Medecin sans frontiere ta fitar, sun nuna cewa mutanen da ke matuƙar buƙatar agajin gaggawa ya haura 500,000. Wasu ‘yan gudun hijira da BBC ta zanta da su, sun ce su na cikin mawuyacin hali na karancin abinci. Har ta kai sukan shiga daji su debo tafasa dan su ciyar da ‘ya’yan su, amma halin da suke ciki ya munana su na tsananin bukatar taimako. To sai dai kuma yunkurin da akan yi don taimaka wa ‘yan gudun hijirar da ke bukata kan ci karo da matsaloli, musamman yadda almundahana kan dabaibaye harkar rabon kayan agajin. A kwanan nan ma, rahotanni sun ce an karkatar da manyan motocin abincin da a watan Fabrairu gwamnati ta ba da umarnin kai wa Jihar Borno don tallafa wa ‘yan gudun hijirar. Sanata Muhammad Ali Ndume dan majalisar dattawa ne mai wakiltar kudancin Jihar ta Borno, ya shaidawa BBC cewa ana gudanar da bincike kan mutumin da ya yi awon gaba da kayan abincin ‘yan gudun hijirar. Kuma tuni hukumar EFCC ta shiga lamarin, dole ya fuskanci hukunci idan aka same shi da laifi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.