yadda zaka bude massingers biyu A waya daya

0 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shafin zumunta na facebook, ya kaddamar da wata
dama ga masu amfani da wayoyin Android. Yanzu
dai duk wayar da ke amfani da kimiyyar android,
za’a iya bude account biyu a lokaci daya,
musamman masu kokarin amfani da damar aika
sakon gaggawa “messenger” mutane kan iya bude
shafufuka biyu daga daya zuwa daya duk a kan
waya daya. Ana iya kara wani account a kan wayar
batare da mutun na cikin shafin shi na facebook
ba, kawai mutun kanyi amfani da shafin aika
sakon gaggawan kadai, idan bukatar shiga shafin
baki daya bata kama ba. Kuma ana iya amfani da
wannan damar na messinja don yin bidiyo call
wato mutun yaga mutun. Idan kuwa har mutun
nada damuwa dangane da wasu zasu iya shiga
cikin account din shi don yi mishi binciken asiri, da
zarar mutun ya zo shiga daya daga cikin account
din, za’a bukaci ya saka sunan shi da kuma
lambar sirri wanda shi kadai ya sani. Hakan ba zai
bama wani damar shiga ba sai wanda yake da
masaniya da ya dace. Idan kuwa wani yayi kokarin
yimaka kutse shafin facebook zasu aika maka da
wani sako, da cewar ko kai ne kake kokarin shiga,
wanda daga bisani idan ka amsa tambayoyin dai-
dai sai abaka damar shiga kai tsaye.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.