Watakilla Rashin yin aurena da adam zango Alkhairi ne Inji Nafisa

0
A wata hira da mujallar yanar gizo ta Kannywoodscene ta yi da harshen turanci da fitaciyya, hazika kuma kyakkyawar jaruma NAFISA ABDULLAHI a fagen daukar shirin LABARINA (wani jerin wasan kwaikwayo da ake haskawa a talabijin da a turance ake kira da “TV series”) na babban darakta Aminu Saira. Jarumar ba ta yi kwaren baki ba wajen warware abubuwa da dama da masoyanta da ma dukkanin masu bibiyar harkar fim din Hausa za su so su sani. Ga yadda hirar ta kaya: A matsayinki na wacce ta ke taka rawar babbar jigo a shirin fim din Labarina, me za ki fada mana gama da fim din? Fim din Labarina ya zo da wata Nafisa Abdullahi a wani matsayi wanda ban taba taka irinsa ba a dukkan finafinan da na taba yi a rayuwata. Haka kuma ina tabbacin dukkanin jaruman shirin na Labarina za su tabbatar maka da cewar fim din ya ba su wani matsayi wanda su da ‘yan kallo za su so su gani. Labarin fim din Labarina ya zo da abubuwa masu ban qaye da ko shakka za su burge ‘yan kallo. A gaskiya ina matukar son hawa matsayi irin wanda ba a saba gani na akan su ba, haka kuma na san ‘yan kallo za so gani na ina taka irin wannan matsayin To, Dan Yi Mana Takaitaccen Bayani Game Da Matsayin Da Ki Ka Hau A Shirin. Na fito a matsayin Sumayya a fim din, kuma ita Sumayya ta kasance wacce soyayya ta yi ta danawa tarko kuma Sumayyar ta yi ta fadawa. Sumayya ta yi tsintar kanta a cikin soyayyar samari, amma sai a kowace soyayya ya kasance tana fitowa cike da bakin ciki sakamakon yaudararta da masoyan da ta amincewa suka yi ta yi mata. Na taba hawa irin wannan matsayi kamar sau daya zuwa biyu, amma yadda rayuwar Sumayya ya kasance a fim din Labarina wani salo ne sabo ko ni a wurina da ma ‘yan kallo A Ciki Sababbin Fuskokin Da Suka Fito A Fim Din Labarina, Wa Ya Fi Burgeki? A gaskiya dukkanninsu sun burgeni, don sun yi kokari. Amma akwai wata ta musamman wacce kokarinta ya kai tsaiko. Wacce a ganina ta cancanci jinjina sakamakon yadda ta gabatar da aikinta cikin hazaka kamar wata kwararriya ko gogaggiya. Wannan jaruma kuwa ita ce Rukayya. Ta fito a matsayin kawata tun ta yarinta. Ta burge ni ne saboda yadda ko kadan bata rude ba. So tari za ka ga jarumai a kokarinsu na kawo zancen da aka daura su fada wata fitowa, sai kaga sun gaza bayyana yanayin da ake bukata da bayyana ko na farin ciki, ko bakin ciki, ko raha, ko fada da dai sauransu. Sai ka ga, ga dai abinda su ke fada na bakin ciki ko bacin rai ne, amma yanayin fuskar bai nuna haka dari bisa dari ba. Amma ita wannan Rukayya, a gaskiya ta yi kokari wajen hade kalamanta da yanayinta a yayin daukar shirin Labarina kamar ba fim din ta na farko ba. Akwai jita-jitar da ke yawo a gari na cewar kin zabi aikin Labarina akan aikin Rahama Sadau na Rariya (Dariya) Kai! Ikon Allah!! A gaskiya jita-jita ce kuma kai ma kasan yadda mutane suke. Gaskiyar magana ita ce, na fara aikin Labarina wata uku kafin Rahama ta zo min da maganar fim din Rariya, sai na fada mata cewa, ina aiki fim din Labarina kuma za mu dau lokaci kafin mu gama. Saboda haka samun damar fitowa a shirin Rariya ya ta’allaka ne da akan yadda darakta na (Aminu Saira) ya bari na ke fitowa a wasu finafinan. Na fadawa Rahama cewa, in har na samu dama zan yi aikinta, amma in ban samu dama ba, ina fata za ta fahimci yadda hali ya zo ne. Kuma ina da tabbacin Aminu Saira ya yi wa daraktan fim din Rariya wannan bayanin da na yi maka yanzu. Saboda haka kawai wani ya yi tunanin saboda wani dalili na daban ne na ya sa ki zuwa aikin Rahama wannan rashin adalci ne. Babu yadda za a yi na bar aikin da na fara yi har ya yi nisa na shiga wani aikin na daban. Babu wani abu da ya saba da ka’idar aiki a nan kuma babu wani abu na rashin jituwa anan, sai dai kuma in har mutum ya kudirce wani abin na daban a zuciyarsa Bayan shirin fim din ki na kashin kanki wato Guguwar So, shin kina da burin sake aikin wani shirin? Eh, akwai finafinai biyu da nake aiki akai, amma shirin bai yi wani nisa ba tukunnaFim din Guguwar So labarin soyayya ne, menene ra’ayinki dangane da soyayya? Ra’ayi na game da soyayya shine: Soyayya ta zamto Soyayya ba So ba. Ma’ana ta zamto kowane bangare na sadar da ita ga abokin soyayyarsa. A ganina, ko dai mutum ya kasance a cikin soyayyar da ta ke aiki ko kuma mutum ya hakura kawai in har soyayyar da ya sadar ba ta dawowa. A ganina, kawai ka so mutum yadda ya ke ba tare da ka yi kokarin canja shi ba shine hakikanin so Who are you in love with now? Da wa ki ke soyayya? Ehhh.. (Murmushi).. akwai wani a zuciyata. Amma ya kamata kuma ka san cewa ba zan fada maka wanene shi ba ko kuma wani bayani akansa a yanzu Kwanakin baya ke da Adam Zango kun fito kun bayyana soyayyarku a kafafen yada labarai. Sai kuma bayan ‘yan kwanaki kadan Adamun ya auri wata daban, ko za ki iya fada mana me ya faru? To, na dai san ka san cewa duk wasu masoya suna da wasu sirrika da ya ke nasu ne na kashin kansu da basa iya bayyana su ga wasu. Ba zan iya fada maka abinda ya faru tsakanina da Adamu ba saboda wani abu ne tsakaninmu, sai dai in baka manta a hirar da na gabatar a wancan lokacin cewa na yi Allah ya zaba mana mafi alkhairi. Saboda haka, watakila rashin yin auren namu shi ne mafi alkhairin. A lokuta da dama za ka samu soyayya ba ta bullewa zuwa ga aure Amma Har yanzu kina son sa? Ba ma soyayya a yanzu, amma duk da bama tare, ba yadda za ka yi ka ce dari bisa dari mun cire junanmu a rayukanmu tun da ba yadda mutum zai iya cire son wani a ransa dare daya Yanzu ya ya ki ke ji da ya yi aure? Ba wani sabon abu bane a tare da ni. Ba wani abinda ke damuna. Irin haka na faruwa da masoya a ko’ina a fadin duniya. Abu mafi muhimmanci shine a duk lokacin da za ka shiga soyayya ka tabbata ka shirya abkuwar irin haka musamman ma mu da mu ke idon duniya. Rashin auren Adamu ba zai zama karshen rayuwata ba. Kamar yadda ka ke gani, Adamu ya yi aure, ni kuma ga shi ina ci gaba da rayuwa Me ‘Yan Kallo Za su tsammata daga gareki? Shirina na gaba zai zama babban shiri ne kuma abin mamaki. ‘Yan kallo za su ganni cikin wani matsayi da ba su saba gani na hau irinsa ba Wani abu ne ba za ki taba mantawa da shi ba tun bayan shigarki masana’antar Kannywood? Ehh.. Wannan lokaci ko yanayi shine kafin da kuma bayan na yi fim din Sai Wata Rana. Fim din ya sa na sanu a duniya duk da kasancewa ta bakuwa a masana’antar amma sai fim din ya yi karbuwar da duk inda na je babu maganar da ake sai na fim din Sai Wata Rana da kuma rawar da na taka a fim din Kin yi nasarar lashe kambin jarumar jarumai a bikin karrama jaruman Kannywood sau biyu a jere. Ko menene sirrin? Daga Allah ne sai kuma rawar da taka a finafinan da suka ba ni damar lashe kanbin. Ba na son na nuna halin rashin kankan da kai, amma nasarata ta samo asali daga yadda na ke zabar finafinan da zan fito a ciki a ‘yan kwanakin nan. Wasunsu ba lalle ne su samar min wani kanbi ba, amma dai naka zabi fim daya cikin goma da suka zo gabana. Irin finafinan da na ke zaba kuwa sune finafinan da na ke ganin za su daukaka darajata a sana’ance Wadanne abubuwa ne suke bambamce ke da sauran jarumai mata? A gaskiya ni ban sani ba. Watakila wasu za su iya bayyana bambamcin. Wasu da dama na dauka cewa bani da lokacin mutane ko ma na kaina, a’a, ba haka abin ya ke ba sam. A gaskiya ni a yanzu ma nake jin dadin kasancewar ni Kina da wani sako ga masoyanki? Ina matukar gode musu tare da yi musu fatan alkhairi. Ina musu fatan Allah ya basu abinda suke so duniya da lahira.