Wani uba ya cinnawa ”ya’yansa wuta

0

A wani lamari mai matukar ban tsoro da ban Tausayi, wani uba mai shekaru 27 ya cinnawa kanshi wuta tare da iyalinsa da suka kunshi
matar shi da ‘yayan su biyu.

Wannan abu ya faru ne a yankin Tirunelveli da ke kasar Indiya a ranar Litinin da ta gabata.

Uban mai suna Esakimuthu dai sai da ya bulbula galan din kalanzir a jikin iyalin na shi kafin ya cinna masu wuta.

Rahotanni sun bayyana cewa Eskimuthu ya na fuskantar matsanancin matsi daga wajen wani da ya ke bin bashi, a sakamakon haka ne ya aikata wannan abu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Matar shi mai suna Subbulakshmi mai shekaru 27, diyarsa Mathi Saranya mai shekaru 4 da Akshaya Bharanitha ‘yar wata 18 da haihuwa
duk sun kone.

Duk da cewa ‘yan sanda sun garzaya da su asibiti, ba su dade a can ba suka rasu.

Shi kuwa Esakimuthu da ya samu kuna mai tsananin digiri 75 ya na cikin matsanancin hali.

©alummata