Wani sanata ya fasa kwan dake tsakani IGP da Matar Shugaban kasa

0 4

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Sanata Misau ya tona asirin Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Kasar

Hamma yace ‘Yan Sanda sun ba Matar Shugaban kasa motoci

Ana dai ta kumfar baki tsakanin Sufetan ‘Yan Sanda da Sanatan

Rikicin Sufeta Janar na ‘Yan Sanda da Sanatan Bauchi Isa Hamma Misau yana cigaba da canza fasali a yanzu a Kasar.

Labari ya kai gare mu na cewa Sanata Isa Hamma Misau ya fasa kwan Matar Shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari da Sufeta Janar na ‘Yan Sanda Ibrahim K. Idris a Majalisa inda yace an ba Uwargidar Shugaban kasar wasu
kyaututtuka.

A cewar Sanatan Matar Shugaban Kasa Buhari ta nemi kyautar motoci daga hannun Jamia’an ‘Yan Sanda wanda Ibrahim Idris yayi wuf ya bata manyan motoci kirar jeep na Toyota Prado har 2 duk da ba ya cikin kasafin kudin Hukumar a ranar.

Matar Shugaba kasar ta nemi dogayen motoci ta hannun dogarin ta wanda Sufetan ‘Yan Sandan ya aika mata zuka-zukan motoci 2.

A cewar sa ma dai akwai wasu badakala iri-iri da Sufetan ‘Yan Sandan ya tafka.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Yanzu haka dai IG na ‘Yan Sandan zai bayyana a Majalisa.

Aisha buhari kenan matar shugaban kasa.
Sanata isah hamma misau da kuma IGP wato Ibrahim k. Idris.
©naijhausa

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram