Wani mutum ya kashe kansa ta hanyar fadawa rijiya a Kano

0 2

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Wani mutum dan shekaru 45 mai suna
Balarabe Haruna ya kashe kan shi ta hanyar
yin tsalle cikin rijiya.

Mutumin wanda ke zaune a unguwar
Hausawa sabon titi a Kano ya aikata abun ne
bayan da ya cewa matarshi da ‘yayan shi 10
su dan bashi guri ya na bukatar hutu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mutumin ya
yi fama da cutar Malaria a makon da ya
gabata, amma har ya ji sauki kafin abun ya
faru.

Iyalin malam Balarabe sun ce ba shi da wata
alamun tabin hankali kuma har yanzu kansu
a daure ya ke game da musabbabin aikata
wannan abu.

Dan mamacin na fari mai suna Balarabe
Mahmud ya shaidawa manema labarai cewa
abun ya faru ne da misalin karfe biyu na
ranar Asabar.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Ya ce sun bar gidan ne bayan da mahaifinsu
ya ce su ba shi guri zai huta, amma da suka
dawo sai suka neme shi suka rasa.

Ya ce sai daga bisani suka ji motsi a cikin
rijiya, lamarin da ya sa suka kirawo ‘yan
kwana kwana.

Yayin da yake tabbatar da faruwan lamarin,
daraktan hukumar kwanakwana a Kano,
Mohammad Rilwan, ya ce sun isa gidan ne
da misalin karfe 3 na rana.

Ya ce a mace suka ciro mutumin daga cikin
rijiyar.

Source: arewaclass.com.ng

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram