Wani Mutum Ya hau karshen Sabis ya fado

0 71

Click to subscribe my channel

Wani bawan Allah da ba a bayyana sunansa ba ya hau kololuwar karfen sabis na bankin Wema da ke Eluwure junction a kan layin Sango-UI a garin Ibadan kuma ya daka tsalle ya fado ya mutu nan take.


Wani shaidan ido mai suna Tosin Alabi ya bayar da labarin yadda lamarin ya faru. “Ya shigo harabar bankin ta baya ne kuma ya hau can saman kololuwar karfen sabis din. Ya kwashe misalin mintuna 30 kafin ya daka tsalle ya fado a rufin bankin.”

Daya daga cikin abokan mamacin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce abokinsa ba mahaukaci bane kamar yadda wasu mutane ke tsamani, ya kara da cewa marigayin abokinsa ne na kut da kut kuma akwai alamar tambaya a kan abinda ya faru dashi.

KARANTA WADANNAN;
1 of 96

Mahaifiyar marigayin, Mrs Alaba ta ce yaron ta bashi da tabin hankali inda ta kara da cewa duk abinda ya sanya ya kashe shi ba kankanin abu bane.

“Mun dawo daga addu’o’in dare kuma kammala karya kummalo, sai muka fara nemansa ashe ba mu sani ba ya tafi ya kashe kansa. Da na bashi da tabin hankali kamar yadda wasu ke tunani sai dai ni ban fahimci abinda ya tunzura shi ya kashe kansa ba.”

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Gbenga Fadeyi ya ce bankin sun kira su da jami’an kwana-kwana domin a ceto mutumin amma daga bisani aka gano ya riga ya mutu. Fadeyi ya ce an kai gawar marigayin zuwa asibitin Adeoyo domin binciko dalilin mutuwarsa.

Click to subscribe my channel