Wani matashi yayiwa uwar sa fyade

0 232

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Wani matashi yayiwa uwar sa fyade,mataahin ya yi wa surukarsa fyade.

Wani dan shekara 32 mai suna Shekani David ya shiga hannun hukuma bisa kama shi da laifin yi wa mahaifiyarsa da surukarsa fyade a jihar Kaduna.

Shekani wanda ya shahara wajen aikata fyade a yankin karamar hukumar Kaura dake jihar Kaduna, an kama shi ne bayan da labarinsa ya isa wurin shugaban ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, inda shi kuma ya umarci kwamandan jami’an binciken manyan laifuka domin yin bincike kan lamarin.

KARANTA WADANNAN;
1 of 6

Bayan an kama Shekani ya tabbatar da yi wa mahaifiyarsa mai shekaru 65 fyade tare da surukarsa har sau biyu.

Ya ce bai san me yake gusar masa da hankali ba a duk lokacin da ya kudiri yin fyaden.

“Ni manomi ne kuma matata ta jima da rabuwa da ni saboda yawan yi wa tsoffi fyade da nake yi.

Na kan yi hakan ne a duk lokacin da na sha barasa. An sha duka na a kan wannan lamari amma na kasa kama kaina”, cewar Shekani.

©hausazone

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram