Wani mallami ya durkawa daliba ciki a makaranta

0

Ma’aikatar ilimin jihar Neja a Nijeriya ta bayyana dakatar da Malam Mohammed Mohammed, mataimakin shugaban daya daga
cikin makarantun sakandire mallakar gwamnatin jihar, sakamakon samunsa da a ka
yi da laifin takarkarewa wajen dirkawa wata daliba ‘yar aji uku na sakandire mai suna Faith
Danjuma ciki.

Babban sakataren ma’aikatar ilimin jihar Neja, Alhaji Yahaya Garba ne ya bayyana manema labarai hukuncin da ma’aikatar ta dauka, inda ya ce tuni aka sanar da babban akanta na
jihar shawarar da kwamitin ladabtarwar hukumar makarantun sakandire ta jihar ta bayar a rahotonta kan binciken lamarin na a
sanya mai laifin a matakin rabin albashi.

A ranar 28 ga watan Maris din wannan shekarar ne ma’aikatar ilimi ta jihar Neja ta samu rahoton Malam Mohammed ya yi wata
daliba ‘yar aji uku a makarantar da ya ke a matsayin mataikakin shugaba ciki, inda da samun rahoton ne ma’aikatar ta yi umarni da a kafa kwamitin ladabtarwa a makarantar.

Makarantar ta kafa kwamitin mutum 8 bisa jagorancin mataimakiyar shugabar makarantar ta biyu, Zainab Kolo.

An kuma umarci kwamitin da su bayar da shawara a rahotonsu kan hukuncin da za a yi wa wanda a ke zargi in har an same shi da
laifin aikata laifin:
“Bayan kammala bincike, kwamitin ya tabbatar da cewa dalibar ta samu juna biyu kamar yadda gwajin babban asibitin Minna ya tabbatar.

Bincike ya tabbatar da cewa dalibar na da cikin mako 7 da kwanaki 6 a ranar da aka gudanar da binciken;Binciken ya tabbatar da cewa ana sa ran dalibar za ta haihu a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, 2017 (yau kenan)”

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Rahoton kwamitin ya shawarci hukumomi da a tilasta Malam Mohammed da ya dauki nauyin
kulawa da dalibar da abinda za ta haifa.

Rahoton ya shawarci hukumomi da a mayar da Malam Mohammed makarantar dalibai maza
zalla.

Babban sakataren ma’aikatar ilimi, Alhaji Yahaya Garba ya ce, ma’aiaktar ta sake kafa wani kwamitin karkashin jagorancin Madam Eunice Gana a matakin hukumar kula da makarantun sakandire don sake yin nazari
akan lamarin Rahoton wannan kwamiti na biyu ya tabbatar
da cewa Malam Mohammed Mohammed ya tabbatar da cewa shi ne ya yi wa dalibar ciki.

Saboda haka ne ma ma’aikatar ilimi ta gaggauta dakatar da Malam Mohammed tare da sanya shi akan rabin albashi har zuwa lokacin da gwamnati za ta yanke hukunci
akansa.

Tuni dai aka tura wani sabon mataimakin shugaban makaranta a wancan makaranta don ya maye gurbi Malam Mohammed.

Credited by alummata