Waka a bakin mai ita: Menene gaskiyar zargin lalata da ake yi a yan matan Kannywood?

0 12

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Waƙa a bakin mai ita: Menene gaskiyar
zargin lalata da ake yi a yan matan
Kannywood?

Batun lalata da yan matan a Kannywood
ya abu ne daya dade ana tattaunawa,
inda jama’a ke nuna yatsa ga yan Fim
din, yayin da su kuma a nasu bangare
suke musantawa.

A wasu lokutta ma ana yi musu zargin
akwai yan luwadi da yan Madigo duk a
cikinsu, amma a nan BBC Hausa tayi hira
da wasu sanannu a harkar ta Fim,
wadanda suka yi bayanin yadda lamarin
yake.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Rahoton majiyar Arewafresh.com ta
bayyana tun bayan fitar wani bidiyo na
wata yar Fim yayin da take lalata da wani
saurayinta a shekarun baya ne jama’a
suka daura ma yan Fim din karan tsana,
inda hakan yayi sanadiyyar gwamnatin
Kano haramta yin Fim na wani lokaci.

nywood ana samun zarge zargen
Furodusoshi na neman yan mata kafin su
saka su cikin fina finansu, amma dai ba’a
samu wata da tayi kokarin fitowa ta
bayyana hakan ba, in banda wata
fitacciyar jaruma daya data bayyana ma
majiyar mu hakan.
Ita dai wannan jaruma ta nemi a boye
sunanta, ta bayyana ma majiyar ta mu
cewa jiga jigan Kannywood da dama sun
nemi sun yi lalata da ita kafin su bata
Fim, amma ta ki, inda tace Ali Nuhu ne
kadai bai taba neman ta ba da niyyar
lalata.

Ita ma wata jaruma a fina finan
Kannywood, Hauwa Waraka ta shaida
cewa duk dayake ba’a taba nemanta da
wannan bukata ba, amma gaskiya ba zata
kawar da yiwuwar hakan ba, sakamakon
kowa da halinsa ya shigo Kannywood.

Shima Ali Nuhu da aka tuntube shi cewa
yayi ba shi da masaniya ko kadan da
faruwar irin wannan abu, inda yace “A
gaskiya ban taba ganin wadda aka ce an
yi lalata da ita gabanin a sanya ta a Fim
ba, kuma ma har kwamiti muka kafa dake
da alhakin lura da hakan.”
Daga karshe majiyar ta tattauna da
shahararren Furodusa, Aminu Saira,
wanda yace “Wannan batu ba gaskiya
bane, don kuwa da ace da gaske ne, da
yan matan da suka gabata a Indostri sun
koka. Kuma da dama daga cikinsu sun yi
aure.”
Sai da wani darakta ya shaida ma
majiyar Arewafresh.com cewa sanadiyyar
irin badakalar dake cikin Kannywood yasa
yake janye jikinsa daga cikinta.

©24wikis

Get real time updates directly on you device, subscribe now.