Wadan da sukayi belin Nmdi kanu suna tsaka mai wuya

0 5

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

A Najeriya, mutanen uku ciki har da wani dan Majalisar dattawan kasar da suka yi belin Shugaban kungiyar ‘yan ware ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu na tsaka mai wuya.

Hakan ya biyo bayan rashin bayyanar sa a gaban kotu ranar Talata, inda mai shari’a Binta Nyako
ta bada umurnin su kawo shi.

Sanata Enyinnaya Abaribe da Immanuel Madu da kuma Torchokwu Uchendu sune suka yi belin Mr Kanu wanda ake yi wa shari’a aKotun tarayya da ke Abuja kan zargin cin amanar kasa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Shi dai lauyan Mr Kanu, Mr Ifeanyi Ejiofor ya shaida wa kotu cewa bai san inda wanda yake kare wa yake ba

Mai shari’a Binta Nyako ta ce matukar wadanda suka tsayawa Mr Kanu suka kasa kawo shi gaban kotun, za su rasa Naira miliyan 100 da suka ajiye cikin sharuddan belin.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram