Wacecce Mawakiya Queen ZeeShaq?

0 99

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

WACE CE QUEEEN ZEESHAQ

Zainab ishaq Muhammad wadda aka fi sani da queenzeeshaq, ta kasance matashiyar mawaqiyar gambara Watauga (Hausa hip-hop ), kuma ta kasance mace ta farko a kano da ta fara wannan salon waqar, kuma mace ta 2 a arewa kwata.

An haifi queenzeeshaq a garin kano, a unguwar brigade da ke qaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Queenzeeshaq, ta yi makarantar firamare a wata makaranta mai suna NURUL-HUDA primary school, daga bisani tayi qaramar sakandire GGSS yankaba, in da ta dora da sakendiren yammata ta GGSS gwagwarwa ta kuma kammala a shekarar 2011, mawaqiyar ta ci gaba da karatunta na boko a kwalejin Shari’ah ta AMINU KANO COLLEGE OF ISLAMIC ND LEGAL STUDIES, Kano, in da anan ne ta karbi shedar N. C. E a shekarar 2017.

A bangaren ilimin addini, mawaqiyar ba a Barta a baya ba, ta yi makarantu daban-daban na addini wadda suka hada da:
qudus islamiyya litahfizul Quran, manarul huda, sautus-sunnah, nurul-huda tahfeez da sauransu, in da ta samu damar sauke alqur.ani mai girma a shekarar 2007 da 2010.

Queenzeeshaq ta ce, ta fara waqa ne a qarshen shekarar 2016, in da tayi waqoqi da dama.

Mawaqiyar ta ce dalilin shigarta waqa, ya kasance tana so ne ta ke ayka saqon ta na fadakarwa ga Al.umma masu yawa cikin sauqi.

Queenzeeshaq ta ce, bata shiga waqa domin neman suna ba, ta shiga ne domin fadakar da yan.uwanta Al.umma da kuma nishadantar dasu.

Queenzeeshaq ta samu damar halartar taruka da yawa, kuma ta samu lambobin yabo da yawa.

Daga cikin waqoqinta akwai :

Lokaci

KARANTA WADANNAN;
1 of 2

Tsumagia

Naseer

Kukan kurciya

Anatare

Hantsi

Akwai dalili

My king

Dasauransu.

Mawaqiyar ta ce, a koda yawshe tana farinciki da masoyanta, kuma tana alfahari da soyayyarasu gareta.

Sahihi tarihin ta ke nan daga gare ta muka samu wannan tarihi.

Idan kana bukatar wakokin duk muna da su a wannan shafi namu

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram