Tsayuwar Arfa: Mafi muhimmancin aikin Hajji

0 4

Click to subscribe my channel

Aci gaba da aikin hajjin bana, kimanin mahajjata
miliyan daya da rabi ne suka taru a filin Arfa a ranar
Lahadin nan, wanda shi ne aiki mafi muhimmanci a
aikin hajji a kasar Saudiya.
Mahajjatan sun taru ne tun daga fitowar rana a filin
Arfa, yayin da suke ci gaba da gudanar da addu’o’i
da karatun Al-Qur’ani mai tsarki.
A filin Arfan ne ma’aiki, Annabi Muhammad (S.A.W)
ya yi hudubarsa ta karshe kafin ya bar duniya.
Aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan
Musulunci biyar, da ake kwadaitar da Musulmai
masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.
A ranar Asabar ne rahotanni suka ce, a karon farko
cikin shekaru talatin da biyar, shugaban malamai na
kasar Saudiya, Abdul Aziz al-Sheikh, ba shi ne zai
gabatar da hudubar da aka saba yi kowacce
shekara ba lokacin aikin Hajjin saboda rashin lafiya.
Hakan kuwa ya biyo bayan takaddamar da
kalamansa suka janyo ne, lokacin da ya ce ‘yan
kasar Iran ba Musulmai ba ne.
Ya dai yi kalaman ne bayan shugaban addini na
kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya soki yadda
Saudiya ke tafiyar da shirye-shiryen aikin Hajjin.
Iran ta ki tura ‘yan kasarta aikin Hajjin na bana, a
maimakon haka, sai ta amince ‘yan kasar tata su je
wani aikin ibadar a birnin Karbala na Iraki ranar
Asabar.
Zaman dar-dar tsakanin Saudiya da Iran ya karu
bayan turmutsitsin da aka samu bara a wajen aikin
Hajji a Saudiya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar
mutane 2426, wadanda suka hada da Iraniyawa
464, a cewar wasu alkaluma wadanda ba na
hukuma.
Saudiya da Iran din ba su da wata dangantaka ta
diflomasiyya, sannan suna yawan samun sabani
akan abubuwa da suka shafi yanki, wadanda suka
hada da rikicin Yemen da Syria.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Click to subscribe my channel