Tirkashi dan Banga ya harbe kansa

0

Wani dan sintirin Isan Gona mai suna Ahmadu Maikare ya harbe kan shi har lahira a yayin da yake gwajin sabuwar layar hana harsashi huda mutum.

Wannan ya faru ne a kauyen Dubul, da ke karamar hukumar Matazu, a jihar Katsina.

‘Yan sintirin Isan Gona Hoto: Daily Trust Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Katsina, DSP Gambo Isah, ne ya baiyana wa manema labarai wannan al’amarin.

Ya ce har yanzu ana nan ana
bincike.

Hakan ya auku ne a yayin da ‘yan
sintirin suka taru a gidan shugaban su, Sama’ila Rabi’u, domin bikin karrama sabbabin wadanda aka diba aiki a cikin su.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Maikare ya tashi tsakiyar jama’a yana tallwmata layun.

Ya daura su a jikin sa yana sunbatun ‘yan bori, kana ya dau
bindiga yar harbi kan shi. Nan take
dalma ta kai shi lahira.

Nan take duk ‘yan taron suka arce, sai ‘yan uwan sa ne suka zo suka dauki gawar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook Page