Tauraron Dan Adam zai taimaka wajen kididdigar talauci

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Masu bincike a Amurka sun ce sun gano wata hanya kididdige yaduwar talauci ta hanyar amfani da bayanan tauraron dan-Adam. Masana kimiyyar na jami’ar Stanford sun yi amfani da kwamfuta don gano ma’aunan ci gaban tattalin arziki, irin su tituna da gine-gine a hotunan da tauraron dan-Adam ya dauka a kasashen Afrika biyar. Sun kwatanta wadannan bayanai da wadanda aka tattara ta hanyar amfani da tsofaffin hanyoyi kamar safiyo. Sun kuma gano cewa manhajar kwamfuta na iya hasko yankunan da ke fama da talauci kamar tsofaffin hanyoyin, ko ma fiye da su. Masu binciken na fatan wannan sakamako zai taimaka wa hukumomin bayar da agaji wajen fuskantar da taimako inda ya fi dacewa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.