Tarihin margayi Sarkin Kano-Ado Bayaro

0

Marigayin Sarkin Kano Ado Bayaro ya rasu ranar juma’a 6 ga watan Yuni na shekarar 2014 bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Kafin rasuwar sa, marigayin ya shafe tsawon shekaru 51 kan gadon mulkin Kano. A tarihin kasar hausa yana daya daga cikin sarakuna mafi daraja da karfin iko kuma shine sarki mafi tsawon shekaru a kan gadon sarautar mulki.

Alhaji Ado Bayero wanda aka nada da sarautar Kano a cikin jamhoriyar farko na shekarar 1963 ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Marigayi yana daya daga cikin sarakunan gargajiya da suka yi tsayin daka wajen farfado da martaban kasar hausa ga bainar jama’a duba da yadda yake jagorantar hawan daba wanda ke janyo jama’a da dama daga kasashen duniya daban-daban.

KARANTA WADANNAN;
1 of 3

kafin ya hau gadon mulki, yayi aiki a matsayin jami’in dan sanda kuma yayi aiki a matsayin ma’aikacin bankin da aikin diflomasiya inda ya zama jakadan Nijeriya zuwa kasar Senegal.

Ya rasu ya bar yara da jikoki, cikin yaran shi akwai Wamban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Sunusi Ado Bayaro da sauran Yaran Sa.

Muna Aduar Alla ya jikan Sa yayiwa Yaran Da ya bari AlBarka.

AMEEN