Tarihin Abdullahi Umar Ganduje

0

TAKAITACCEN TARIHIN MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO DR. ABDULLAHI UMAR GANDUJE OFR.(Khadimul-Islam).

KARATU
An haifi Dr. Abdullahi Umar Ganduje Ranar 25 ga watan Disambar shekara ta 1949, Dr. Ganduje ya fito daga tsatson Masarautar garinsu, Maihifinsa Alhaji Umar Shi’aibu Shi ne; Dagacin kauyen Ganduje, dake karamar Hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kanon Nijeriya.

Dr. Abdullahi Ganduje. A matakin farko ya fara karatunsa na neman Ilimin Addinin Islama na Al-Qur’ani, da kuma halartar Makarantar Islamiyya A kauyen Ganduje, inda ya samu horo a fannin ilimin Mahammadiyya a matakin farko.


Daga bisani ya garzaya zuwa mazaunin babbar Shalkwatar karamar hukumarsa ta Dawakin Tofa inda ya fara karatunsa na zamani na Makarantar Firamare a Shekarar 1956 zuwa 1963. Dr. Ganduje ya halarci Shahararriyar babbar Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Birnin Kudu a Shekarar 1964 zuwa 1968. A kokarinsa na bunkasa iliminsa Dr. Ganduje ya halarci manyan Makarantun gaba da Sikandire da daman gaske, Inda ya mallaki Shaidar Shahadar Malanta ta kasa(NCE), A Babbar Kwalejin horas da Malamai ta Kano (Advance Teachers’ College Kano) A tskankanin shekarar 1969 zuwa 1972. 


Har-ila-yau Dr. Ganduje ya sake halartar Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Zaria) don samun mallakar Shaidar Digiri na daya A fannin ilimi da kimiyya (Bachelor degree in Science Education) daga shekarar 1972 zuwa 1975. Dr. Ganduje ya samu shaidar digirinsa na biyu A fannin Ilimi da Kimiyyar halaye da dabi’un Dan Adama (Masters degree in Applied Educational Psychology) A Jami’ar Bayero, Kano A Shekarar 1979. Sannan kuma ya sake koma wa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya daga Shekarar 1984 zuwa 1985 don sake wani sabon Digirin na biyu har-ila-yau a fannin Al’amuran Gudanarwa (Masters in Public Administration).

Bai gaza ba, sai da Dr. Ganduje ya halarci Jami’ar Ibadan dake Kudu-maso-Kudancin Nijeriya don samun Shahadar Digirin Digir-gir, wato Digiri na uku (PhD) a fannin Al’amuran Gudanarwa (Public Administration) A Shekarar 1989 zuwa 1993.

FANNIN AIKI
Dr. Ganduje bai tsaya kawai a samun horo da kwarewa fannin ilimii da harkokin gudanarwa ba kadai, har-ila-yau yana da kwarewa a 6angarori biyu. Ya fara aikinsa a matsayin Malami a Shekarar 1975 A kwalejin Ole (Ole College) A yankin Kudu-maso-kudancin Nijeriya, lokacin da yake gudanar da hidimar bautawa kasa(NYSC).

Bayan ya kammala Bautar kasa (NYSC)ya samu Aiki A Gwamnatin Jihar Kano, A karkashin Ma’aikatar Ilimi, a matsayin Malami a matakin na biyu (Education Officer II) A Shekarar 1976, kuma dai a wannan Shekarar ta 1976 ya kuma koma wa Kwalejin horas da Malamai mai Zurfi ta Kano (Advance Teachers’ College, Kano), A Matsayin Babban Malami ko lakcara mai bada horas wa a fannin Ilimin da Kimiyyar halaye da dabi’un Dan-Adam (Educational Psychology).

KARANTA WADANNAN;
1 of 2

Bayan Shekaru biyu da fara aiki Dr. Ganduje ya fara koyarwa A Jami’ar Bayero, Kano A Shekarar 1978 a matsayin babban Malami ko lakcara (Lecturer I). Bayan ya kwashe tsawon shekaru biyar yana koyarwa a matsayin Malami Mai horas wa, Dr. Ganduje ya fara aikinsa na Al’amuran gudanarwa A Kamfanin “Nornit Limited Kano” A Matsayin Manajan Sashe (Personnel Manager) A Shekarar 1979 Zuwa 1981.

A Shekarar 1981 Dr. Ganduje ya fara aiki da Hukumar Bunkasa Birane ta Tarayya “Federal Capital Development Authority” A matsayin Helima ko Ofisa mai kula da harkokin gudanarwa (Admin Officer) daga nan kuma ya samu damar darewa Zinariyar Kujerar matsayin Daraktan Bincike, kididdiga da Tsare-tsare (Director Planning, Research and Statistics) A Shekarar 1993. Bayan ya kwashe Shekaru goma sha bakwai (17) yana aiki da Hukumar “FCDA” Dr. Ganduje ya rike Mukamai a 6angarori da daman gaske, wanda suka hada da: Sakataren Ci gaban Yankin Kwalli ( Development Secretary of Kwalli Development area); ya kuma ta6a zama Jami’i mai kula da yankin Abaji (Sole Administrator, Abaji Area Council); ya kuma ta6a zama Shugaban Yankin Gwagwalada (Chairman, Gwagwalada area Council). Har-ila-yau an kuma nada shi a matsayin Babban Sakatare Mai kula da Sulhu da biyan Diyya a babban Birnin Tarayya Abuja (Executive Secretary of FCT resettlement and compensation).

An kuma nada Dr. Ganduje A matsayin Kwamishina na Ma’aikatar Aiyuka, Gidaje da Sufuri Na jihar Kano (Hon. Commissioner Ministry of Works, Housing and Transport Kano State) A Janairun Shekarar 1994 Zuwa Nuwanbar, Shekarar 1998.

FANNIN SIYASA
Dr. Ganduje’s A burinsa na hidimtawa al’ummarsa bai tsaya nan ba har-ila-yau ya fada cikin harkokin siyasa gadan-gadan, inda ya shiga Shudaddiyar Jam’iyyar Siyasar mutanen Nijeriya ta N.P.N. (National Party of Nigeria) A Jamhoriya ta biyu(2), inda ya yi aiki a matsayin Mataimakin magatakarda na jihar kano (Assistant Secretary) daga shekarar 1979 Zuwa 1980. Dr. Ganduje ya shiga Jam’iyyar P.D.P. (People Democratic Party) inda ya tsaya a matsayin dan takara me neman salhalewar Jam’iyyar ta P.D.P A matsayin Gwamnan jihar Kano, kafin daga bisani ya zama Mataimakin Gwamna, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso A tsakanin Shekarar 1999 Zuwa 2003, har-ila-yau kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano daga Shekarar 2003 Zuwa 2007 (Hon. Commissioner for Local Government). Ya kuma zama Me ba wa Mai girma Ministan Tsaron tarayyar Nijeriya Shawara akan harkokin Siyasa (Special Adviser Political).

Dr. Ganduje ya ta6a zama Mamba a Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Nijeriya (Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA). An nada Dr. Ganduje A Matsayin Shugaban Makarantar Kimiyya ta Nijeriya dake jihar Ado Ekiti (Chairman Federal Polytechnic, Ado Ekiti) A Shekarar 2008. Sannan kuma an ta6a nada Ganduje a matsayin Babban Sakatare na hukumar yankin Chadi Basin dake Jamhoriyar Chadi(Executive Secretary Lake Chad Basin Commission at Ndjamena, Chad Republic).

Dr. Ganduje Ya zama Jagora ko jigo wurin kare martabar Kabilarsa da yarensa na Fulani da Makiyaya inda aka za6e shi a matsayin Shugaban Kungiyar TABITAL FUAKU na Kasa (TABITAL FUAKU NIGERIA) Kuma Jami’i mai kula da yankin Yamma da Yankin Afirka ta Tsakiya (In-charge East and Central Africa sub-region). Dr. Ganduje ya kuma ta6a bada tasa gudunmawar a matsayin Mamba a taron karawa juna ilimi na gyaran al’amuran Siyasar Nijeriya( Member, Nigerian Political Reforms Conference) A Shekarar 2006.

A Shekara ta 2011 Zuwa 2015 ya sake zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi Karkashin Darikar Siyasar Kwankwasiyya. A ranar 29 ga watan Mayun Shekarar ta 2015 an Rantsar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam) da Mataimakinsa Prof. Hafizu Abubakar A Matsayin Gwamna da Mataimaki.

FANNIN TAIMAKON MARAYU DA MABUKATA:
Dr. Ganduje A kokarinsa da tausayinsa ga Al’umma hakan tasa ya himmatu wurin taimakawa raunana marasa karfi, da Marayu da Mabukata. Saboda haka ne ma ya kafa wata Cibiya mai Suna GANDUJE FOUNDATION.