Tab shirin Npower shirirri tane…adeyanju

0 0

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Shugaban wata kungiyar ‘yan kishin
Najeriya, Deji Adeyanju, ya bayyana shirin nan na samar da aiki ga na N-power, karkashin gwamnatin shugaba Buhari, a matsayin shiririta.

Da yake bayyana ra’ayin sa a wani shiri da gidan talabijin na Channels ke gabatarwa kullum, Adeyanju, ya ce rage radadin talauci ba daya yake da samar da aiki ba.

Deji Adeyanju Hakazalika, Adeyanju, wanda ya a baya ya taba rike mukamin darektan sadarwar zamani na jam’iyyar PDP ya
zargi shugaba Buhari da yin makarkashiya ga kasuwancin wadanda keda burin yin takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

“Ban ga takamaimai aikin da shirin na N-power ya samar ba ” a kalaman Adeyanju.

Adeyanju ya baiwa gwamnatin shugaba Buhari shawarar ta mayar da hankali wajen koyar da matsa sana’o’in dogaro da kai ta hanyar basu horo karkashin kulawar bankin kula da harkokin masana’antu ba wai ba wa matasamarasa aiki kudin kashewa ba.

©naij

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram