Sule Lamido ya fadi abin dake zuciyar sa a jam’iyar PDP

0 9

Click to subscribe my channel

Mun samu labari daga Jaridar Daily
Trust cewa tsohon Gwamna Sule Lamido ya fadawa Jam’iyyar PDP cewa zai yi takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Sule Lamido na shirin tsayawa takara 2019 Tsohon Gwamnan na Jihar Jigawa ya bayyanawa ‘Yan Jam’iyyar PDP cewa zai tsaya takarar Shugaban Kasa a
zaben 2019 a wata takarda da aikawa jam’iyyar ta bakin Umar Kyari.

Lamido yace ya cancanci tsayawa takara zabe a Kasar.

Sule Lamido a takardar ya koka da
yadda abubuwa su ka tabarbare a
Najeriya yace shi ne zai dawo da Kasar kan saitin da magabata su kayi mata.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Sule yace shi zai sharewa ‘Yan Najeriya hawaye idan ya samu tikitin Jam’iyyar na zaben 2019.

Alhaji Sule Lamido dai yace ba mamaki wasu su nemi kujerar Shugaban kasar a Jam’iyyar amma ya nuna a shirya yake don kuwa ya isa.

Irin su Gwamnan Jihar Ekiti su na neman tsayawa takara a Jam’iyyar.

©naij.hausa.com

Click to subscribe my channel