Sojoji sun kama mutum 1,240

0 2

Click to subscribe my channel

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ce rundunar sojin Najeriya ta kama wasu da ake zargi
‘yan Boko Haram ne su 1,240, a yayin wani samame da dakaru suka kai a dajin Sambisa.

Manjo-Janar Lucky Irabor, wanda ke jagorantar aikin tsaro na Operation Lafiya Dole, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a wani sansanin soji da ke Maiduguri.
Irabor ya ce mutum 413 daga cikin wadanda ake zargin maza ne manya, sannan 323 manyan mata
ne, sai yara maza 251 da kuma yara mata 253.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Ya ce, “Muna yi masu tambayoyi, domin mu tabbatar ko ‘yan Boko Haram ne, saboda mun san
babu yadda za a yi wani da baya cikin kungiyar Boko Haram, ya zamana yana cikin dajin na
Sambisa.”

Click to subscribe my channel