Sojin sama sun musanta zargin kisan yan matan chibock

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rundunar sojan sama ta Nigeria ta musanta ikirarin Boko Haram cewa, hare-haren da suke kaiwa sun kashe wasu daga cikin ‘yan matan Chibok. Sojan saman Najeriyar sun ce, ‘yan Boko Haram sun ƙirƙiri shiri ne kawai domin nuna cewa, hare-hare ta sama ne suka kashe wasu ‘yan matan Chibok. Rundunar sojan tana mayar da martani ne ga bidioyon da Boko Haram suka fitar ranar Lahadi inda suka yi ikirarin cewa, harin sojan saman Nigeria ya kashe da dama daga cikin ‘yan matan Chibok da suka sace. A shafinta na Facebook rundunar sojan saman Najeriyar ta kuma ce, ‘yan Boko Haram sun ɗauko hotunan wasu gawarwaki ne suka tsara a bidiyon. Sojan saman sun ƙara da cewa, wurin da ‘yan Boko Haram suka nuna bai yi kama da wurin da aka kaiwa hari ta sama ba. Rundunar sojan saman Najeriyar ta kuma sanya bidiyo a Facebook da ya nuna yadda suke amfani da na’urori masu hangen nesa dake fayyace mayaƙan Boko Haram kafin a kai musu hari ta sama. Bidiyon ya kuma nuna yadda ake bincike mai zurfi, da tattara bayanan sirri kafin a kai kowanne hari da jiragen yaƙi. “Muna da na’urori na zamani da matakai masu yawa dake tantancewa sosai kafin mu kai hari ta sama da rana, ko cikin dare. A duk lokacin da muke da shakku to muna dakatar da kai hari har sai mun tabbatar da abokan gaba ne kafin mu kai hari ta sama”, in ji rundunar sojan saman ta Nigeria. Dan haka ne sojan saman na Nigeria suka ce, ‘yan Boko Haram sun yi amfani da bidiyon da suka fitar domin yaudarar jama’a. Ranar Lahadi ce dai ‘yan Boko Haram suka fitar da bidiyo inda suka ce, hari ta sama na sojan Nigeria ya kashe wasu daga cikin ‘yan matan Chibok. Hare-hare ta sama dai sun yi tasiri wajen cin karfin ‘yan Boko Haram.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.