Sojin Nijeriya Sun Cafke Shugaban Karamar Hukumar Mafa Ta Jihar Borno Da Laifin Taimakawa ‘Yan Boko Haram

0

Rundunar sojan Nigeria ta cafke shugaban riko na karamar hukumar Mafa a jihar Borno tare da wani kwamandan Boko Haram da ya bai wa mafaka a gidansa dake unguwar Gida Dubu kan hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Dakarun sojan sun kama Alhaji Shettima Lawan Maina da kwamandan Boko Haram din da ba a bayyana sunansa ba ne ranar Asabar da daddare bayan da makobtansa suka tsegunta musu cewa ya boye shi a gidansa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

An dai jima ana zargin wasu daga cikin ‘yan siyasar jihar Borno da kulla alaka da mayakan Boko Haram.