Sirrin kiwan kaji inji bill gate

0 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Attajirin Ba’Amurken nan, Bill Gates ya ce yana
shirin taimaka wa al’umomin da ke kasashe
marasa galihu da dubban kaji da nufin bunkasa
kiwonsu.
Ya yi amanna da cewa kiwon kajin zai taimaka
wajen inganta rayuwar jama’a, tare da rage
talauci, musamman ga mata wadanda za su yi
dawainiyar kiwon su.
Attajirin ya ce akwai sirri sosai a harkar kiwon
kaji, saboda za su dinga hayayyafa suna ninka
yawansu.
Mr Bill Gates ya ce zai aiwatar da shirin ne a
kasashen da ke shiyyar Afirka ta yamma.
A cewarsa, binciken da ya gudanar ya nuna cewa
a duk lokacin da aka raya ‘yan tsaki goma, to
sukan yi albarkar da ta kai dala 10,000 a duk
shekara.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.