Shugaba Buhari Baya Karya-Minista

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ministar kudin Najeriya ta Zainab Ahmed ta kare shugaban kasar Muhammadu Buhari kan ayyukan da ya ce gwamnatinsa na aiwatarwa sa’ilin gabatar da kasafin kudin kasar na 2019, a zauren majalisar dokokin kasar.

Ministar kudin ta ce babu yadda za a yi shugaban kasar ya fadi abinda ba gaskiya ba ne.

A cewar ta “Shugaban kasa mutum ne mai gaskiya kuma tsayayye, ba yanda za a yi ya ce an yi abu wanda ba a yi ba.”

A cikin hirar da ta yi da BBC, ta ce dukkanin ayyukan da shugaban kasar ya fada suna cikin kasafin kudin shekarar 2018, wanda zai tsaya a watan Yunin shekarar 2019.

KARANTA WADANNAN;
1 of 89

Ta kuma ce an sake sanya ayyukan cikin kasafin kudin shekarar 2019, domin tabbatar da cewa an kammala su.

An dai samu rudani a lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a zauren majalisar dokokin ta Najeriya.

Inda wasu wakilan majalisar suka rinka katsalandan a lokacin da shugaban kasar ke jawabi, musamman a lokacin da yake bayani kan nasarorin gwamnatinsa.

Sun rinka cewa ‘karya’, ko ‘a ina?’, wasu kuma na cewa ‘ba haka ba ne.’

Wasu sun yi wa Buhari ihu a lokacin gabatar da kasafin 2019
hakikin Malaka bbchausa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.