Shekau ya fadi inda yake a sambisa in gaskia ne

0 1

Click to subscribe my channel

Rundunar sojin Nigeria ta kalubalanci shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da ya fadi in da yake a dajin Sambisa in da gaske ne ikrarin da ya yi cewa sojojinta ba su fattake su daga can ba.

A ranar Alhamis ne dai wani faifan bidiyo ya bulla dake nuna Shekau din yana musanta kalaman da
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a makon jiya cewa dakarun kasar sun fatattaki mayakan Boko Haram daga dajin na Sambisa.

Sai dai rundunar ta bayyana bidiyon da cewa farfaganda ce kawai kuma za ta yi nazari a kansa.

”Ba wani wuri da suke yanzu a dajin Sambisa, kuma in ya ce suna nan, ya gaya mana a ina ne yake a Sambisa ai yaranmu na wurin.”

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

In ji Birgediya-Janar Rabe Abubakar kakakin hedikwatar tsaron kasar cikin wata hira da BBC.

A faifan bidiyon mai tsawon mintuna 25 dai, Shekau ya yi ikrarin cewa “Muna nan da ranmu da lafiyarmu.

Babu wanda ya kore mu daga wani wuri.”

Click to subscribe my channel