Sharu khan ya gindaya shardi a kan yarsa

0 10

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shahararren Jarumin nan na Bollywood, Shah Rukh Khan ya gindaya wasu dokoki ga duk
saurayin da zai ce ya na son ‘yar sa Suhana mai shekaru 16.

Jarumin wanda uba ne ga ‘yaya uku; Aryan Suhana da Abram, ya bayyana cewa yana matukar son ‘yayan nasa kuma yana sanya
masu ido ya kula da su yadda ya kamata.

A wata Hira da ya yi, jarumin ya bayyana cewa duk saurarin da zai ce yana son ‘yar sa
to sai ya:

1. Kasance ya na da aikin yi

2. Fahimci cewa shi Sharukh Khan baya son shi

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

3. Ya samo lauya mai tsaya masa

4. Ya sani cewa Suhana Gimbiyar
Shahrukhan ce, ba wata kyauta ba da ya ciwo

5. Ya sani cewa shi Sharukh Khan ba ya tsoron komawa gidan yari

6. Ya sani cewa duk abunda ya yi wa yarsa.sai ya rama mata.

Jarumin dama dai ya dade yana sanya ido.akan irin samarin da ke kusantar ‘yar ta sa, kuma da alama ya yi wannan magana ne
domin ya razana su.

Jarumin wanda a kwanan nan ya samu lambar yabo a matsayin gwarzon uba na kasar Indiya ya bayyana cewa tun da ya taso
kawo yanzu ya koyi darussa da dama musamman a gurin matan da ya ke harkokin fim da su, ya ce wannan darussa su suka sa ya damu akan ‘yarsa kuma ba zai ba wani namiji ya bata mata ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.