Sarkin Muslmi yayi watsi da rabon gado

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A Najeriya mai alfarma sarkin musulmi, ya yi watsi da kudurin dokar da zai kawo daidaito tsakanin mace da namiji wajen rabon gado.

Muhammad Sa’ad Abubakar yace ba za a amince da duk wata doka da za ta yi wa dokokin addinin musulunci karan tsaye ba, inda maza su ke daukar kaso mafi rinjaye akan mata idan aka zo batun rabon gado.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

A watan Oktoba ne, kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta amince da kudurin dokar, wadda masu fafutuka suka ce za ta taimaka wajen rage nunawa mata banbanci.

Tun da fari ‘yan majalisa sun yi watsi da kudurin dokar, su na cewa ba ta dace da addini da kuma al’adun wasu ‘yan Najeriya ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.