Salman khan zai shiga sahun masu haihuwa ba aure

0

Da alamar shahararren jarumin fina finan India Salman Khan, zai shiga
cikin mutanen da suke haifuwa ba tare da aure ba.

Lallai wannan ba sabon labari ba ne cewar, Salman na kin yin aure tun da dadewa.

Sai dai jarumin yace zai haifu amma duk da hakan ya makara.

Kowa na sane da yanda jarumin ke
sha’awar samun haifuwa kuma yace zai cika shekaru 52 a cikin watan Disamba wannan shekara, don haka shi kansa na ganin lokaci yayi.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Rahotannin sun nuna cewar mahaifiyar Salman Khan tana so ya samu abin haifuwa, yace akwai yiwuwar nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa zai nemi wacce zata haifu masa.

Dan wasan yace yana sane da idan ya haifu a yanzu, hakan na nufin a lokacin da dansa zai cika shekaru 20 wato shi kuma ya samu shekaru 70.

Salman Khan yace lallai zi yi hakan
saboda ya farantawa iyayensa rai.

Tusshar Kapoor shine ya fara wannan salon haifuwa ba tare da aure ba a masana’antar final finai ta Bollywood a shekarar 2016 yayin da ya haifi dansa Lakshya, bayan haka darekta Kara Johar ya biyo sawu inda shi kuma ya samu yan biyu da suka hada da Yash da Roohi.

©voa