Rundunar yansandan kano ta hana kwankwaso aurear da zawarawa

0 5

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

‘Rundunar ‘Yan Sanda ta Hana Kwankwaso Aurar da Zawarawa a Kano A yau ne ya kamata Gidauniyar tsohon gwamnan jahar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ta gudanar da shirin ta na daura auren zawarawa guda 100 a filin sukuwa da ke jakar Kano. Sai dai al’amarin bai yiwu ba a sakamakon hana taron da Rundunar ‘yan sandan jahar Kanon ta yi. ‘Yan sandan sun ce sun soke daurin auren ne bayan da su ka samu wasu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu mutane na shirin kawo yamutsi a lokacin taron. Har kawo yanzu gidauniyar ba ta ce komai ba game da wannan al’amari Wannan abu ya auku ne a dai dai lokacin da gwamantin jahar Kano, a karkashin shugabancin dokta Abdullahi Umar Ganduje ke cikin tantance zawarawa da ‘yan mata guda 10,000 da za ta yi wa aure. Tun a watan Maris din bana ne bayan da mahaifiyar gwamna Ganduje ta rasu, dangantaka ta kara tsami tsakanin Kwankwason da Ganduje.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.