Rundunar ‘Yan Sanda Jahar Kano Ta Kama Masu Fyade 570 a Shekarar Nan

0

Kwamishinan ‘yan sanda jahar kano Rabiu Yusuf ya ce ‘yan sanda sun kama mutane 570 da ake zargi da laifin fyade a fadin jahar daga watan Janairun shekarar nan izuwa yanzu.

Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar DSP Magaji Musa Majiya wanda rundunar ta fitar.

Sanarwar ta ce an kawowa rundunar
kararrakin fyade guda 547, na kisa guda 86, na fashi da makami guda 72 da kuma na satar mutane guda 43 a wannan shekara.

Banda mutane 570 da aka kama akan laifin fyade, rundunar ta ce ta kama mutane 119 da ake tuhuma da laifin satar mutane, da kuma mutane 117 da ake zargi da laifin fashi da makami.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Haka kuma rundunar ta ceto mutane 27 da aka sace, ta kuma karbo makamai 78 da alburusai 651 da kudade da adadinsu ya kai naira 2, 750,000 daga hannun masu satar mutane.

Ta ce ta kwato makamai 64, alburusai 634, mashinan hawa 52 da Keke Napep guda 15 daga hannun ‘yan fashi a wannan shekara.

Sanarwar ta bayyana cewa an samu raguwar manyan laifuka a jahar Kano a wannan shekara idan aka kwatanta shi da na shekarun baya.