Rundunar sojin Nigeria ta kwato jirgin Burtaniya

0
Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta samu ƙwato wani jirgin ruwan Burtaniya na ‘yan kasuwa daga hannun ‘yan fashin teku. A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce, cikin gaggawa jirgin yakinta ya je wurin da lamarin ya faru a cikin teku wanda bai wuce nisan mil 20 daga Bonny ba, a ranar Laraba. Kuma sojoji sun samu ceto ma’aikatan jirgin wadanda suka kulle kansu a cikin wani daki, kuma suna cikin ƙoshin lafiya. Tuni dai rundunar ta ce ta fara bincike domin gano yadda aka yi yunkurin fashin jirgin ruwan da bai yi nasara ba. A baya-bayan nan fashin teku ya fara ƙaruwa a gabar teku ta yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya.