Rundunar sojin Nigeria ta chafke bature a cikin yan boko-haram

0 3

Click to subscribe my channel

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta cafke wani
Bature wanda har yanzu ba a san ko dan
asalin wace kasa bane a cikin Dajin Sambisa
a yayin da dakarun ke ci gaba da tsefe dajin.
Wannan batu dai ya zo ne bayan da rundunar
ta samu nasarar murkushe sansanin ‘yan
Boko Haram na karshe da ke cikin Sambisa a
ranar Juma’ar da ta gabata.
Jaridar Daily Trust ta rahoto wani soja da aka
yi ba ta kashin da shi inda ya ke cewa a halin
yanzu ana gudanar da tambayoyi a kan
Baturen kuma yana bayar da hadin kai.
Sojan ya tabbatar da cewa a halin yanzu babu
wani Kwamandan Boko Haram da ya rage a
cikin Dajin Sambisa saboda sojoji sun karbe
ikon dajin gaba daya.
daga

alummata.com

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Click to subscribe my channel