Rundanar sojin Nigeria Ta saki Ahamed Bolari

0 0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rundunar sojin Najeriya ta sallami, Ahmed Bolori bayan ta yi masa wasu tambayoyi. Ahmed Bolori dai na daya daga cikin mutum uku da rundunar ta ba da sanarwar cewa tana nemansu ruwa-a-jallo. Hakan ya faru ne bayan wani hoton bidiyo dauke da ‘yan matan Chibok da kungiyar boko haram ta fitar, kasancewar sai da suka samu bidiyon kafin kungiyar ta sanya shi a intanet. Ahmed Bolori ya shaida wa BBC cewa sojojin sun ce kuskure ne suka yi wajen bayyana cewa suna nemansa ruwa a jallo ba, alhalin suna son ya je ne ya taimaka dan a samu shawo kan matsalar da ake fuskanta ta Boko Haram. Bolori yace babu wani batanci da sojojin suka yi masa, kuma sun tattauna kan batutuwan tsaro da sauran su, kuma sun sake shi ne bisa sharadin duk lokacin da suka bukace shi zai gabatar da kansa. Sai dai ya ce bai san inda ‘yan Boko Haram su ke ba ko kuma ‘yan matan Chibok suke ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.