Rikici Tsakani ‘Yan Jam’iyyar APC da PDP a Edo

0 1

Click to subscribe my channel

Mazauna kauyen Okugbe da ke karamar
hukumar Estako East a jahar Edo sun shiga
tashin hankali a sakamakon rikici da ya barke
tsakanin ‘yan jam’iyyar PDP da APC wanda ya
haifar da rasa dukiyoyi a yankin.
Rahotan ya bayyana cewa a safiyar yau ne
‘yan jam’iyyar PDP suka bazama titinan
kauyen suka shiga rikici da ‘yan jam’iyyar
APC. Majiyarmu ta bayyana cewa abun har sai
da ya fi karfin jami’an ‘yan sandan yankin,
yayin da matasan suka fara fasa motoci da
sauran dukiyoyi mallakar ‘yan jami’yyar APC.
Haka kuma rahotan ya bayyana cewa matasan
sun afka ofishin ‘yan sanda inda suka saki
wasu ‘yan bangan siyasa ‘yan jam’iyyar PDP
da ‘yan sanda suka tsare.
Akwai kishi kishin cewa wannan rikici na da
alaka da zaben gwamnan jahar da aka daga
daga jiya Alhamis zuwa gobe Asabar 10 ga
watan nan.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Click to subscribe my channel