Rikicin jami’yyar PDP yaki karewa

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Nigeria ta samu kanta a cikin tsaka mai wuya bayan manyan kotuna biyu na kasar sun bayar da umarni masu cin karo da juna kan shugabancinta. Wata babbar kotu a Abuja ta haramta wa jam’iyyar yin babban taronta da za a yi a fatakwal a ranar Laraba. Hakan na zuwa ne bayan wata babbar kotun da ke zamanta a Fatakwal ta bayar da umarnin a yi taron. Tun bayan da PDP ta rasa mulkin Najeriya a shekarar 2015 ne jam’iyyar ke fuskantar rikici na cikin gida, lamarin da ke kara dagulewa. Hakazalika yunkurin daidaita bagarorin da ba sa ga maciji da juna na Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi ya ci tura.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.