Rikici tsakanin makiyaya da manoma

0

Hankula sun soma kwantawa a gundumar Yelwa-Tai ta karamar hukumar Ardo Kola da ke jihar Taraba biyo bayan fadan tsawon kwanaki uku da ya barke sakanin manoma da Fulani makiyaya wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka biyu da kone-konen dukiyoyin jama’a.

Da yake tabbatar da abkuwar tashin hankali na baya bayan nan, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ASP David Shall ya ce rikicin ya samo asali daga zargin da bangarorin ke yiwa juna na saka shanu a gonakin manoma tun ba su kammala girbi ba inji manoman yayin da makiyayan a na su bangaren ke tuhumar ana sanyawa shanunsu guba duk lokacin da suka yi barna.

Kawo yanzu dai kakakin hukumar ‘yan sanda ya ce kome ya lafa kuma an aike da karin jami’an ‘yan sanda masu kwantar da tarzoma don hana rikicin yaduwa zuwa wasu sassa na jiha.

Ya ce hukamar ta kama mutane hudu da take tuhuma da hannu a tashin hankalin.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Wani mazaunin Yelwa-Tai Mal. Baital Hussen ya shadawa sashin Hausa ta waya cewa jama’a sun koma bayan kauracewa yankin don sake gina muhallan su da aka lalata sanadiyyar rikicin .

Mal. Abdullahi Maikasuwa wanda ya
ziyarci kauyen Yelwa-Tai bayan lafawan tashe-tashen hankulan ya ce an dauki tsauraran matakan tsaro a yankin da kuma kewaye da ba a taba ganin irin sa a baya ba don gudun yaduwar tashinbhankalin zuwa wasu sassa na jihar Taraba.

Wakilinmu Sanusi Adamu ya yi kokarin ji daga bakin mai baiwa gwamnan jihar Taraba shawara kan harkokin tsaro Kanal Wunukhen Angyo mai ritaya wanda ya kai ziyarar gani da ido yankin da tashin hankalin ya shafa bayan ya shaida masa yana kan hanyarsa ta wayar selula ya cutura.