Rashin sani yakai dillallin wiwi motar yan sanda

0 3

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Wani wanda ake tuhuma da dillancin tabar wiwi yayi wani abin takaici, bayan da fada  cikin wata mota cikin hanzari dauke da daurin tabar ta wiwi 1,000 a tare da shi, kafin ya fahimci cewa motar ta ‘yan sanda ce.

Jami’an ‘yan sanda a Denmark sun ce
mutumin na sauri ne ya isa gidansa a lokacin da yayi wannan batar basirar.

Wannan lamarin ya auku ne a Christiana,
wani yankin babbban birnim kasar da akak kafa shi a shekarun 1970, kuma sanannen cibiyar cinikin haramtattun kwayoyi ne a kasar.

‘Yan sandan sun ce zasu gurfanar da shi a gaban alkali, inda zai iya fuskantar dauri a gidan yari idan aka same shi da laifin cinikin tabar wiwi.

Ga yadda rahoton na ‘yan sandan ya bayyan lamarin: “A jiya, wani dilan tabar wiwi daga Christiana wanda ke cikin saurin domin komawa gidansa ya fada bayan wata motar tasi.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Amma ya sha mamaki bayan da ya
fahimci cewa motar ‘yan sanda ce ya shiga.”

“Jami’an ‘yan sanda dake cikin motar sun yi murna da ganinsa, tun da yan dauke da
daurin tabar ta wiwi kimanin guda 1,000.”

Dauka da dillancin tabar wiwi laifi ne a kasar ta Denmark.

Jami’an ‘yan sanda sun yi ta kai samame
cikin unguwar Christiana a watannin da suka gabata, domin neman zakulo dillalan  haramtattun kwayoyi da tabar wiwi.

©bbc

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram