Rasha zata dau mataki akan Amuruka

0

Rasha ta sha alwashin daukar mataki a kan korar jami’an diplomasiyyarta 35 daga Amurka, bisa zargin kasar da yin katsalandan a cikin zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a watan jiya.

Firayim ministan Rasha Dmitry Medvedev ya ce gwamnati mai barin gado ta Shugaba Obama za ta kare wa’adinta da nuna kiyayya ga Rasha.

Ma’aikatar harkokin wajen Rashan ta ce za a sanar da irin matakin da za a dauka a ranar Juma’a.

Rasha dai ta musanta zargin da ake mata na yin katsalandan a cikin zaben kasar Amurka inda ta kira matakin da Amurkan ta dauka a matsayin maras tushe

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

An dai ba wa jami’an diplomasiyar na Rasha sa’oi 72 su fice daga kasar kuma za a rufe wasu cibiyoyi biyu da suke amfani da su wajen tattara wa kasar bayanan sirri.

Tun ba yau ba dai Shugaba Obama wanda Donald Trump zai gada a ranar 20 ga watan Janairun 2017 ya sha alwashin daukar mataki kan Rasha bisa zargin cewa ita ce ta bayar da umarnin yin kutsen.

Amurka ta ce an shiga cikin akwatunan sakonnin
e-mail na jam’iyyar Demokrat da kuma ofishin kamfe na Hillary Clinton domin bai wa Mista Trump dama.