Qur’anin shekau ya isa hannun Buhari

0

Shugaban rundunar Sojojin Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Lurky Irabor ya mika wa Shugaba Muhammad Buhari ainihin tutar da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ke amfani da ita a cikin dajin Sambisa.

An mika tutar ne a wurin liyafar da rundunar tsaron fadar shugaban kasa ta shirya a Abuja.

Wannan tuta na daya daga cikin ganimar da sojojin suka samu a lokacin da suka fattattaki
‘yan Boko Haram daga dajin Sambisa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Haka kuma sun samu gano Alkur’ani da shugaban na Boko Haram ke amfani da shi wanda shi ma sun mikawa shugaban kasar.