PDP tayabawa Buhari

0 7

Click to subscribe my channel

Babbar jam’iyyar hamayya ta Nigeria PDP ta yaba
wa shugaban kasar Muhammadu Buhari bisa nasarar kakkabe ‘yan Boko-Haram daga dajin Sambisa.

PDP ta ce ta jinjina wa Buhari bisa tsayuwar-dakan da ya yi a yakin da ake yi da ‘yan Boko Haram.
Haka kuma jam’iyyar ta nuna farin ciki kan abin da ta ce ci-gaba da Buhari ya yi a kan kokarin da
gwamnatin Goodluck Jonathan na PDP ta yi a yakin da ta’addanci.

Wata sanarwar da sakataren watsa labaran jam’iyyar Price Dayo Adoyeye ya fitar ta ce nasarar
da aka samu a yakin da ake yi da Boko Haram ta samo tushe ne daga irin kokarin da gwamnatin
baya ta yi, musamman ‘yan makwanni, gabanin gudanar da zaben shuugaban kasa a shekarar
2015.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Sanarwar ta PDP ta kuma jinjina wa sojojin Nigeria
bisa jajircewa a yukurin raba kasar da masu tada kayar baya.

To sai dai PDP ta ce kwace dajin Sambisa ba ya nufin cewa an kammala yaki da ta’addanci, ta yi
kira hukumomin Nigeria su matsa-kaimi wajen kakkabe ‘yan ta’adda daga dazukan kasar da dama
da suka zama wata mafaka ga ‘yan ta’adda.

Ba kasafai dai PDP ke yabawa Buhari ba, kuma a
lokuta da dama tana caccakarsa kan koma baya a
bangaren tattalin arziki.

Click to subscribe my channel