Nigeria zata tattauna da avengers

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ministan albarkatun mai na Nigeria, Emmanuel
Ibe Kachikwu, ya ce gwamnatin kasar za ta yi
tattaunawar sulhu da masu tayar da kayar bayan
da ke kai hare-hare kan bututan mai a yankin
Naija Delta.
Mista Kachikwu ya ce gwamnati za ta yi hakan
ne domin kawo karshen hare-haren da ‘yan
bindigar ke kai wa da suka yi sanadiyyar raguwar
danyan man da kasar ke hakowa.
‘Yan kungiyar Niger Delta Avengers ne suka dauki
alhakin mafiya yawan hare-haren da ake kaiwa a
yankin tun watan Faburairu.
A ranar Talata mataimakin shugaban kasa,
Farfesa Yemi Osinbajo, ya tattauna da jami’an
tsaro da gwamnonin yankin Niger Delta, da nufin
kawo karshe hare-haren da kuma samar da
kwanciyar hankali a yankin.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya Mista
Kachikwu na cewa: ”Za a dakatar da duk wani
aikin soji a yankin na makonni biyu domin
mazauna kauyukan su halarci zaman
tattaunawar”.
A cewarsa, gwamnati tana kokarin samar da
kwanciyar hankali a yankin inda hare-haren ‘yan
kungiyar Avengers ke matukar tasiri a kan hakar
man
Su waye ‘yan kungiyar Niger Delta Avengers?
Avengers sun sake fasa rijiyoyin mai
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan
kammala taron, gwamnan jihar Delta Ifeanyi
Okowa, ya ce an yi taron ne saboda bukatar hada
kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi
domin gano bakin zaren matsalar.
Man da Najeriya ke samarwa ya ragu zuwa
ganga miliyan 1.65 a kowace rana a kan
hasashen da aka yi na ganga miliyan 2.2 a
kowace rana.
Wannan ya sa kasar na tafka asarar biliyoyin
naira a kudaden shigar ta ke samu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.