Nigeria zata kashe kudi kimanin tirilliyon 8.6 a 2018

0 2

Click to subscribe my channel

A yau ne shugaba Buahri ya mika wa majalisa kasafin kudinsa na badi 2018, wanda shine kashi na uku tun karbe mulki daga hannun jam’iyyar PDP.

Wanda kuma yafi kowanne yawan kudi, kusan ninki 3 na abin da PDP ke kasawa.

Shugaba Buhari ya mika wa majalisa kasafin kudin badi na naira tiriliyan tara Naira tiriliyan takwas da digo shida (wato N8.6 Trillion) aka shirya kashe wa a badin.

Kuma kusan dukka kudaden za’a same su ne daga noma, haraji, sayar da mai da makamashin gas.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

An kuma dora bajat din kan za’a
sayar da gangar mai miliyan biyu a duk rana.

A jawabinsa ga majalisar dokin kasar yayin gabatar da kasafin, Shugaba Buhari ya ce gwamantinsa tana tsammanin za ta samu kimanin naira tiriliyan 2.442 daga albarkatun mai, wanda hakan ke nuna an sake samun ragi kan yawan dogaro da mai da kasar keyi.

Sai dai, kusan har mulkin na shugaba Buhari ya kusa kare wa, amma talakka dai bai fita daga kangin talauci ba, sai dai ma karuwa da yayi a wasu wuraren, inda aka sami ci gaba a bangarorin tsaro da noma.

Click to subscribe my channel