Ni Ba Dan Nigeria Bane-Nmadi Kanu

0 52

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

A yau Asabar dinnan ne, shugaban kungiyar ma su kokarin kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ba wa mutane da yawa mamaki, a lokacin da ya bayyana cewa shi ba dan Najeriya ba ne, kuma ba shi da wata alaka da Najeriya. A lokacin da yake bayanin, a gidan Radiyon Biafra, Kanu ya ce zai kalubalanci kotun da ta ba da damar kamo shi a birnin Landan.

Ta faru ta kare: Nnamdi Kanu ya mayarwa da kotu martani, ya ce shi ba dan Najeriya ba ne
KARANTA WADANNAN;
1 of 93

Idan baku manta ba, majiyarmu ta kawo muku rahoton cewa wata Kotun Koli da ke Abuja ta bayar da damar kamo Kanu a duk inda yake, saboda ya ki bayyana a gabanta.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai, Kanu ya ce “duk wani yunkuri da gwamnati ta yi akan kamo shi a shirye ya ke, kuma zamu kalubalanci kowacce kotu a birnin Landan shi da lauyoyinsa. “Sannan kuma ni ba dan Najeriya ba ne, saboda haka shari’arku ba za ta yi aiki a kaina ba, kuma duk wanda ya ke so ya ji dalilina na kin komawa kotu to ya fara tambayar sojojin da su ka je gidana mai su ka je yi?”

#legit

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram